Jakadan kasar Tunisia dake kasar Libya Ridha Boukadi, a jiya Alhamis, ya bayar da tabbacin cewar, wani jami'in diplomasiyya na Tunisia ya bace a Tiripoli, babban birnin Libya.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewar, wasu masu dauke da damarar bindigogi ne, suka yi awon gaba da jami'in diplomasiyyar na Tunisia, to amma Boukadi bai bayyana karin bayanai ba kan maganar sace jami'in diplomasiyyar.
Tabbatar da bacewar jami'in diplomasiyyar na Tunisiar, ya zo a daidai lokacin da gwamnatin rikon kwarya ta Libya ke kokarin karin kariya ga jami'an huldar diplomasiyya na kasashen ketare dake Tiripoli domin tsaron lafiyarsu.
Hakazalika a safiyar Talatar da ta gabata ne, wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba, suka yi awon gaba da jakadan kasar Jordan dake Libya, Fawaz al-Eatan.
A halin da ake ciki dai, Tiripoli na ci gaba da fuskantar matsalolin sace-sacen mutane da fashi da makamai, duk kuwa da cewar, gwamnatin rikon kwaryar ta kasar na ci gaba da gudanar da kokari, ba tare da wata galaba ba, na kwance damarar 'yan bindiga da wasu masu dauke da bindigogi, wadanda suka taimaka wajen rusa gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi. (Suwaiba)