Wasu hare-haren ta'addanci da aka kai a ranar Alhamis da safe a cikin jihar Ouallam dake yankin Tillabery, a yammacin kasar Nijar, sun yi sanadiyar mutuwar mutune tara daga cikin jami'an tsaron kasar na (FDS). An kai wadannan hare-hare a jere da misalin karfe biyar na safe, kan gidan yarin birnin Ouallam, sansanin 'yan gudun hijirar kasar Mali na Manguaize da kuma kan wani ayarin sojojin yankin Tillabery dake sintiri, a cewar wata sanarwar ministan cikin gidan Nijar. Kakakin jami'an tsaro na FDS, kanal Laudru Mustapha ya bayyana cewa, adadin wucin gadin na wadannan hare-hare ya tashi zuwa mutane tara, daga cikinsu, akwai 'yan sanda biyar, jandarma biyu da garda sarki biyu, tare da jikkata wasu mutane hudu. (Maman Ada)