Sojojin Algeria sun kashe a kalla 'yan tsagera 7, tare da kame wani mutum guda a yayin da suke gudanar da ayyukan kare a kan iyakar kasar da kasashen Mali da Libya.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, sojojin Algeria sun lalata wasu motoci biyu, tare da hallaka 'yan tsagera 5 a yayin da suke kokarin tsallake kan iyakar kasar daga Mali zuwa Algeria a kudancin Bordj Badji Mokhtar.
Majiyar ta ce, wani farmakin da sojojin na Algeria suka kai a kan iyaka da kasar Libya ya kashe wasu sojoji 2, tare da lalata mota guda, da kuma amshe wasu muggan makamai.
Tun bayan barkewar tashe-tashen hankula a arewacin Mali da Libya, Algeria ta tura da karin sojoji a kusa da kan iyakokinta da Libya da Algeria, a wani kokarin da take yi na kare kasarta daga kutsen mayaka. (Suwaiba)