in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta Kudu sun dauki niyyar warware matsaloli cikin ruwan sanyi
2014-11-05 14:49:36 cri

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun bayyana niyyarsu a ranar Talata wajen warware wasu batutuwan dake kan tebur cikin ruwan sanyi, musammun ma batutuwan da suka shafi tsaro, ta yadda za su zauna cikin kusanci tare da juna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kasashen biyu sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa bayan shawarwarin da suka gudana a birnin Khartoum a ranar Talata tsakanin shugaban kasar Sudan Omar El-Bashir da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit.

A cewar sanarwar da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka karanta, shugabannin biyu sun jaddada niyyarsu wajen aiwatar da yarjejeniyar dangantaka da kuma warware dukkan batutuwan dake kan tebur domin zaman tare kusa da juna cikin zaman lafiya. Shawarwarin sun mai da hankali kan aiwatar cikin gaggawa da yarjejeniyar dangantaka, da kasashen biyu suka tattabawa hannu baki dayanta, a cewar wannan sanarwa. Haka kuma an sake jaddada matakin kaddamar cikin gaggawa da kafa wani yankin kan iyaka da ba na soji ba tsakanin kasashen biyu. Bangarorin biyu sun cimma ra'ayi daya wajen karfafa hanyoyi da matakan da suka shafi tallafawa da baiwa kungiyoyi masu dauke makamai mafaka tsakanin kasashen biyu.

Mista Mayardit ya isa Khartoum, babban birnin Sudan a ranar Talata a cikin wata ziyarar aiki bisa goron gayyatar takwaransa na Sudan. Ziyarar shugaban kasar Sudan ta Kudu a Khartoum ta zo kwanaki biyu kafin taron kungiyar IGAD a birnin Addis-Abeba na kasar Habasha, da zummar bunkasa kokarin da ake yanzu domin warware rikicin a yankin kudu cikin ruwan sanyi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China