Miliyoyin mutane a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara na saukin samun ruwan sha masu tsabta da kuma abinci mai gina jiki bisa yin amfani da fasahohin kasar Sin masu rahusa, in ji hukumar muhalli ta MDD (UNEP) a ranar Talata.
Kasar Sin ta hada kai da UNEP domin saukaka isar da fasahohi kan kula da albarkatun ruwa da noma dake shafar al'ummomin dake cikin kasashen 16 dake nahiyar Afrika.
Dangantaka dake tsakanin Sin da PNUE kan kula da muhalli ta canji sosai game kyautatuwar hanyoyin zaman rayuwa a Afrika.
Al'ummomi a wadannan kasashe sun fahimci tasirin samun ruwan sha masu tsabta da kuma aikin noma cikin karko, in ji darektan dake kula da reshen muhalli a cibiyar shiyya ta UNEP a Afrika, dokta Mohammed Abdel Monem. (Maman Ada)