Takadama tsakanin Ghana da Cote d'Ivoire game da iyakar kan ruwa za'a warware ta hanyar raba gardamar kasa da kasa, in ji wani babban jami'in kasar Ghana, bayan kasa cimma nasara tsakanin bangarorin biyu wajen daidaita wannan matsala a tsawon kusan shekaru uku ana tattaunawa.
Kasar Ghana ta fara wani shirin neman raba gardama bisa tsarin yarjejeniyar MDD kan 'yancin ruwa, domin ganin an kafa iyakar ruwanta tare da kasar Cote d'Ivoire cikin adalci, bisa gaskiya domin bangarorin biyu, kana kwata kwata, kuma bisa dokar da za ta tilastawa bangarorin biyu girmama matakin kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, in ji ministar shari'ar Ghana kuma babbar alkalin kasar, madam Marietta Brew Appiah-Oppong a ranar Talata da yamma a birnin Accra. (Maman Ada)