Ministan dangantaka da hadin gwiwar kasa da kasa na Afirka ta kudu Maite Nkoana-Mashabane ya bayyana cewa, kasarsa na hadin gwiwar siyasar da ta dace da kasar Sin, wadda kuma za a iya yin amfani da ita wajen shimfida ginshikan cimma manufofin tattalin arziki.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a birnin Pretoria kan ziyarar da shugaba Zuma ya kawo nan kasar Sin daga ranar 4 zuwa 5 ga wata, yana mai cewa, kasar Sin ta amince da bukatar da kasar Afirka ta Kudu ta gabatar mata na kafa yankin masana'antu a kasar, da kuma bunkasa harkokin kimiyya da fasahar kere-kere.
Yayin ziyarar, sassan biyu sun amince kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta shekaru 5 zuwa 10 da gwamnatocin sassan biyu suka sanyawa hannu tun lokacin da aka kammala yarjejeniyar Beijing a shekara 2010.
Karkashin yarjejeniyar, kasar Sin ta amince ta fadada shirin shigo da kayayyakin kasar Afirka ta Kudu kamar masara da tufa zuwa kasuwannin kasar Sin. Har ila kasar Sin ta amince ta taimakawa kasar Afirka ta Kudu wajen horar da ma'aikatanta, shirin ta na bunkasa masana'antu ta yadda sassan biyu za su amfana da juna.
Bugu da kari sassan biyu sun tattauna hanyoyin inganta harkokin yawon shakatawa, ta yadda za a kara zuba jari a bangaren.
Shugaba Zuma da takwaransa na kasar Sin shugaba Xi Jinping sun kuma tabo batun dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC da kasar Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncinsa a shekara 2015.
Idan ba a manta ba kasar Sin ce ta dauki nauyin shirya taron dandalin Afirka ta Kudu a shekarar 2014, dandalin da ya samar da wata kyakkyawar dama ga kasar Afirka ta Kudu wajen nuna irin nasarorin da ta cimma a fannonin tattalin arziki, siyasa da kuma bangaren al'adu. (Ibrahim)