in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya gamsu da ziyararsa a Sin
2014-12-08 14:27:25 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, ziyararsa a kasar Sin a ranakun 4 da 5 ga watan Disamba, ta kasance cikin nasara da alheri.

A cewar wata sanarwar da gwamnatin Afrika ta Kudu ta fitar a shafinta na internet a ranar Lahadi, mista Zuma ya nuna cewa, sakamako mai armashi na wannan ziyara ya kara bayyana kafuwar huldar dangantaka tsakanin Afrika ta Kudu da kasar Sin, musammun ma a bangaren kasuwanci da zuba jari.

Ziyarar ta karfafa hudarmu sosai tare da kasar Sin, a shirya take wajen yin aiki tare da kasarmu domin aiwatar da dukkan shirye shirye da yarjejeniyoyin da muka rattabawa hannu bi da bi, kuma yadda ya kamata, in ji shugaba Zuma.

A yayin ziyarar shugaba Jacop Zuma a kasar Sin, an sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama. Bankin ci gaban kasashen BRICS na daya daga cikin manyan batutuwan da aka mai da hankali kan su a yayin tattaunawar shuagabannin kasashen biyu, haka kuma bangarorin biyu sun amince wajen ganin an kafa bankin da fara aikinsa tun wuri. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China