in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaben majalissar dokokin Tunusia ya yi armashi
2014-10-27 10:25:57 cri

Dubun dubatar al'ummar kasar Tunisia ne suka kada kuri'unsu, yayin zaben 'yan majalissar dokokin kasar da ya kammala a yammacin Lahadi.

Sabanin hasashen kauracewa zaben da a baya aka yi, kimanin kaso 60 bisa dari na daukacin masu kada kuri'ar kasar su sama da miliyan 5 ne babbar hukumar lura da zaben kasar ISIE ta tabbatar sun jefa kuri'unsu.

Wannan zabe dai shi ne na farko tun bayan kaddamar da sabon daftarin kundin mulkin kasar na watan Janairun da ya shude, matakin da kuma ke cikin mafiya muhimmanci, a yunkurin dora kasar kan turbar dimokaradiyya, tun bayan hambarar da gwamnatin shugaban kasar Zine al-Abidine Ben Ali a shekarar 2011.

Yan takara kimanin 13,000 daga jam'iyyu kusan 90 ne dai suka shiga takarar neman wakilcin kujeru 217, a sabuwar majalissar dokokin kasar da za a kafa. Ana kuma fatan bayyana sakamakonsa cikin 'yan kwanaki dake tafe.

Masu fashin baki dai na ganin jam'iyyar Islama ta Ennahda da ta 'yan baruwan mu Nida Tunis ne ke sahun gaba wajen magoya baya, wadanda kuma su ake hasashen za su samu gagarumin rinjaye. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China