Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yiwa kasar Tunisia murna ta gudanar da zaben majalisar dokokin kasar, a inda ya ce, zaben wani babban mataki ne a game da makomar kasar.
Ban ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, zaben majalisar dokokin kasar wanda aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata, ya zamanto wata rana ta tarihi a game da komawa ga kan tsarin damokradiyya a kasar.
Ban ya kara da cewar, zaben ya haifar da dimbin fata na gari, to amma ya ce, har yanzu akwai manyan ayyuka a gaban gwamnatin kasar ta gaba.
A ranar Alhamis mai zuwa ne za'a bayyana sakamakon zaben na farko kuma MDD ta ce a shirya take ta tallafawa kasar ta Tunisia wadda kuma tuni ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 23 ga watan Nuwumba mai zuwa. (Suwaiba)