Mahukuntan kasar Libiya sun ce, dakarun sojin kasar na ci gaba da matsa kaimi, a yunkurin da suke yi na kwace birnin Tripoli daga mayakan 'yan kishin Islama.
Rahotanni daga fadar gwamnatin kasar na cewa, a yanzu haka, sojojin kasar na yiwa birnin kawanya, za kuma su yi amfani da karfi kan duk wanda ya yi kokarin dakile aniyar ta su, ko ya yi kokarin jefa rayukan fafaren hula cikin mawuyacin hali.
Bisa wannan mataki, gwamnatin kasar ta bukaci daukacin kungiyoyin 'yan tada kayar baya da su ajiye makamansu. Kaza lika an bukaci al'ummar kasar da su dauki matakan kalubalantar mayakan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin Islama dake kasar. (Saminu)