in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun Libya ta dage sauraran shari'ar jami'an gwamnatin Gaddafi zuwa 14 ga Disamba
2014-12-01 12:17:37 cri

Wata kotun daukaka kara ta Tripoli, babban birnin kasar Libya, ta dage sauraran wata shari'ar wasu mutane 31 zuwa 14 ga watan Disamba, mutanen wadanda jami'an toshon shugaban kasar ne marigayi Gaddafi.

Wata kafar yada labarai ta Libya da aka yi wa lakabi da Al-Nabaa ta ruwaito cewar, bayan alkalin kotun ya saurari bahasin dimbim lauyoyi masu kare wadanda ake tuhuma, da kuma jawaban wadanda ake tuhumar sai alkalin ya dage zama na goma na sauraren shari'ar kuma hakan ya yi daidai da bukatun lauyoyin wadanda ake tuhuma.

Saif al-Islam wanda da ne na Gaddafi ya kasa bayyana a gaban kotun a karo na biyu a jere saboda matsaloli na tsaro da kuma matsalar da na'urori suka samu wadanda da suna aiki da za'a iya nuno shi daga wakafin da ake ci gaba da tsare shi a garin Zintan.

A halin da ake ciki jami'an tsohon shugaban kasar 37 ne ke fuskantar tuhuma saboda tuhumar su da ake yi da zargin aiwatar da kisan kai da tursasawa masu zanga-zanga a lokacin tashin hankalin shekarar 2011, wadda ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatin marigayi Gaddafi.

Kotun tana kuma tuhumar wadanda ake zargi da kisan kare dangi da kuma kai farmaki kan garuruwa da kauyukan da suka yi zanga-zanga kyamar gwamnatin Gaddafi. Kotun ta kuma yi masu zargin kashe kudaden gwamnati ba bisa ka'ida ba.

A halin da ake ciki dai jami'ai da dama na gwamnatin Gaddafi, ciki har da 'yayan shi maza guda biyu Saif-al Islam da al- Saadi suna ci gaba da kasancewa a kurkuku inda ake zargin su a bisa aikata laifuka da dama. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China