in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tallafin da Sin ke baiwa Afirka ba mulkin mallaka ba ne
2014-12-09 09:54:32 cri

Mataimakin darektan sashen bayar da tallafi ga kasashen ketare na ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin Liu Junfeng ya bayyana cewa, maganar banza ce da rashin shaidu a zargi kasar Sin cewa, tana gudanar da wani nau'i na mulkin mallaka a nahiyar Afirka.

Liu wanda ya bayyana hakan ranar Litinin ya kuma jaddada cewa, kasar Sin tana baiwa sauran kasashe tallafi ne da nufin kawar da talauci, inganta rayuwar al'ummominsu, samun saurin bunkasuwa da kuma karfin dogaro da kansu, matakin da kasar Sin din ke gudanarwa na tsawon lokaci.

Mr. Liu ya ce, kasar Sin na yin hadin gwiwa da nahiyar Afirka ne a fannonin makamashi da albarakatun kasa bisa dokokin kasuwannin kasa da kasa, sannan ta kan ba da galibin tallafi ne ga kasashen ketare a fannonin aikin gona, ba da ilimi, kiwon lafiya, sufuri, sadarwa da kuma samar da wutar lantarki.

Kasar Sin ta tura likitoci 500 da kwararrun kiwon lafiya don yaki da cutar Ebola. Kana a cikin shekaru 50 da suka gabata, Sin ta tura sama da tawagogin ma'aikatan kiwon lafiya 50 wadanda ke kunshe da kwararru sama da 4,000 zuwa kasashen Afirka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China