in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin Sin ya yi kira da a karfafa dangantakar shari'a tsakanin Sin da Afrika
2014-11-14 10:17:11 cri

Mista Gu Shaoming, wani babban masanin harkokin shari'a a kasar Sin, ya yi kiran da a zurfafa huldar dangantakar da ta dace ta fuskar shari'a bisa tsarin bunkasa sabuwar dangantakar manyan tsare tsare tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afrika.

Mista Gu, darektan cibiyar dangantakar al'ummar kasar Sin bisa 'yanci, ya bayyana ganin wani sabon tsarin shari'a na duniya domin gyaren fuska da daidaita tsarin kasa da kasa, haka kuma domin nuna hanya, tabbatarwa da bunkasa huldar dangantakar kasa da kasa da dangantakar shiyya. Kwararren kasar Sin ya yi wadannan kalamai a albarkacin dandalin shari'a tsakanin Sin da Afrika karo na biyar da aka bude a ranar Laraba a birnin Luanda. Dandalin ya tattara kimamin mahalarta dari biyar wadanda suka hada da jami'an gwamnatoci, jami'an shari'a da kwarraru kan ilmin 'yanci da suka fito daga kasar Sin da kuma wasu kasashen Afrika guda tara.

A cewar mista Gu, ya kamata a karfafa dangantakar shari'a tsakanin Sin da Afrika, ta yadda za'a ji muryar kasashe masu tasowa, da kuma kiyaye moriyar juna ta hanyar ba da horo da kuma musanyar ma'aikata. Haka kuma ya jaddada fatan ganin an kafa wata cibiyar shiga tsakani ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika da za'a dorawa nauyin yin aiki kan warware rigingimu a nan gaba dake da nasaba da zuba jari, gina manyan kayyayakin more rayuwa, sauyin yanayi da tsaron abinci, da kuma gabatar da ayyukan shari'a na gari domin huldar manyan tsare tsare da dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China