in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kafofin watsa labarun Afrika da su fuskanci farfagandar yammacin duniya
2014-06-19 10:58:33 cri

Ministan sadarwar kasar Namibiya, Joel Kaapanda ya shawarta a karfafa karfin kafofin watsa labarai na kasashen Afrika domin yin takara tare ko ma samun nasara kan kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya.

A cikin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yayin babban dandali karo na biyu kan dangantakar aikin jarida tsakanin Sin da Afrika, da aka gudana a ranakun Litinin da Talata a nan birnin Beijing, mista Kaapanda ya jaddada cewa, ya zama wajibi, yanzu a kara zuba jari wajen horar da ma'aikatan kafofin watsa labaran kasashen Afrika, da kuma samar da kayayyakin aiki na zamani, ta yadda za su iyar fafatawa yadda ya kamata tare da takwarorinsu na sauran kasashen duniya.

Wannan zai taimaka wa kafofin watsa labarai na Afrika karfin gurgunta farfagandar kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya kan nahiyar Afrika, da kafa wani misalin Afrika mai kyau ga idon duniya bisa matsayin da ya dace da Afrika, in ji wannan jami'in, tare da nuna cewa, dangantaka tsakanin kafofin watsa labarai na kasar Sin da na kasashen Afrika wani muhimmin mataki ne, wajen cimma wannan muradi ta hanyar ba shi kwarin gwiwa da kuma zurfafa shi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China