Mataimakin shugaban cibiyar nazarin harkokin cinikayyar kasa da kasa da hadin gwiwar tattalin arziki ta kasar Sin Li Guanghui, ya ce, ga dukkanin alamu, kasar Sin da takwarorinta na nahiyar Afirka, za su fadada hadin gwiwar dake tsakanin su a fannin tattalin arziki da ci gaba.
A cewar Mr. Li, ziyarar da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kai wasu kasashen nahiyar ta Afirka ta karfafa wannan buri, tare da bude kofar karin damammaki ga kamfanonin kasar Sin wajen zuba jari a nahiyar.
Yayin dai ziyarar da firaminista Li Keqiang ya kammala a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana kudurin da ake da shi, na habaka hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin sassan biyu, musamman a fannoni 6 da suka hada da sashen masana'antu, da na kudi, da yaki da talauci. Sauran sun hada da fannin kare muhallin halittu, da na musayar al'adu da kuma fannin wanzar da zaman lafiya da tsaro.
Kaza lika kasar Sin ta alkawarta tallafawa shirye-shiryen samar da basussuka, domin bunkasa samar da ababen more rayuwa a nahiyar ta Afirka. (Saminu)