A sakamakomn wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a jihar Yobe a yanzu, hukumomi a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nigeria sun rage tsawon adadin dokar hana fitar dare ta awoyi 24 da aka kakaba a garin Damaturu, a inda a yanzu za'a dakatar da fita waje tun daga magariba zuwa wayewar gari.
Wata majiya ta sojoji ta ce, masu tada kayar bayan 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a kan birnin a bangaren yammmacin birnin, wanda ke kusa da kan iyaka da jihar Borno.
Tun dai a ranar Talata ne aka yi shelar dokar ta awoyi 24, to amma sai ofishin gwamnatin jihar ya canza lokacin da dokar za ta yi aiki inda aka mai da daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 na safe, bayan da ya tattauna da hukumomin tsaro dake jihar.
Taron da aka yi ya mai da hankali wajen daukar mataki na magance mummunan harin da aka kai Damaturu. (Suwaiba)