Rahotanni daga Najeriya na cewa, dakarun sojin kasar sun kwato garin Chibok dake jihar Borno daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin runduna ta 7 ta dakarun sojin kanar Sani Usman, ya ce, hakan ya biyo bayan dauki ba dadin da sojojin suka yi da 'yan Boko Haram a ranar Lahadi. Kanar Usman ya kara da cewa, dakarun sojin na ci gaba da gudanar da sintiri, domin tabbatar da raba kewayen yankin da birbishin mayakan kungiyar.
Shi ma a nasa bangare, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade, ya bayyana wa manema labaru cewa, dakarun sojin kasar sun fatattaki mayakan na Boko Haram, tare kuma da kame wasu daga cikin su.
A cikin watan Afirilun da ya gabata ne dai mayakan kungiyar ta Boko Haram suka yi awon gaba da dalibai 276 daga makarantar sakandiren 'yan mata dake garin Chibok. Kuma kawo yanzu mayakan na ci gaba da tsare daukacin su, in ba da kimanin 57 da suka samu kubuta.
Kaza lika mayakan kungiyar na rike da wasu garuruwa da kauyuka sama da 20. Tsakanin shekaru 5 kuma da suka shafe suna kaddamar da hare-haren, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, sun sabbaba hallakar rayukan al'umma da aka hakikance sun kai mutane 10,000. (Saminu)