in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zuba kudi dala biliyan 2 a cikin sabon asusun raya Afrika
2014-05-23 10:21:44 cri

Bankin al'umma na kasar Sin da bankin raya kasashen Afrika ADB sun rattaba hannu a kan yarjejeniya ta kimanin dalar Amurka biliyan biyu domin kafa sabon asusu na fadada zuba jari a Afrika mai suna "Afrika, a girma tare" AGTF.

Wannan shiri na AGTF, ana sa ran za'a samar da shi ne na tsawon shekaru 10, sannan za'a yi amfani da shi tare da kayayyakin da bankin raya kasashen Afirka ADB yake da su wajen aiwatar da ayyuka masu manyan muhimmanci da ma wadanda ba su da su sosai a nahiyar.

Wannan yarjejeniyar, an rattaba hannu a kan ta ne a ranar Alhamis din nan 22 ga wata karkashin jagorancin shugaban bankin ADB Dr. Donald Kaberuka da kuma gwamnan babban bankin kasar Sin Zhou Xiaochuan a lokacin babban taro na shekara shekara na bankin ADB da ake yi a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Muhimmancin wannan rattaba hannu yana da ma'ana mai yawa game da dangantakar kasar Sin da bankin raya kasashen Afrika ADB, in ji Mr. Kaberuka wanda ya kuma lura cewa, Sin, abokiyar Afrika ce wadda ta zuba jari a ababen more rayuwa da kuma ababen halittu.

A don haka sai ya bayyana imaninsa na cewa, nan da shekaru 10 masu zuwa za'a samu dimbin cigaba don alfanu mai yawan gaske wajen inganta rayuwan al'ummar nahiyar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China