in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu ma'aikatan Kenya na gujewa daga gari kan iyaka saboda karuwar hare-haren ta'addanci
2014-12-08 10:52:27 cri

Wasu ma'aikatan gwamnati a kasar Kenya da dama na gujewa daga garin Mandera dake arewacin kasar saboda karuwar rashin matakan tsaro bayan da aka hallaka mutane 60 a cikin makonni 3 da suka wuce.

Gwamnan Mandera Ali Roba, a yayin da yake jawabi ga 'yan jarida ya ce, a yanzu haka wasu malamai 150, sun rubuta takardar iznin ficewa daga garin kuma ma'aikatan ba su tabbacin cewar, za su komo ba.

Shugabannin garin na Mandera sun shaidawa 'yan jarida cewar, an rufe kusan cibiyoyin kiwon lafiya 20, bayan ma'aikatan kiwon lafiya sun fice daga yankin saboda fargabar hare-haren ta'addanci, shugabannnin sun kuma yi kira a kan gwamnatin Kenya da ta taimaka wajen dakatar da ma'aikatan daga gujewa daga yankin.

Gwamnan na Mandera ya ce, halin rashin tsaron da yankin ya shiga ya yi gagarumin tasiri a kan yankin na Mandera, musamman bayan wani hari daga kungiyar Al-Shabaab wacce ta kai harin kwantan bauna a kan wata mota kirar bus kuma ta kashe wasu mutane 28 wadanda ba su bin addinin Islama, kana kuma a wannan makon, kungiyar ta kashe wasu ma'aikata 36 masu hakar ma'adinai. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China