Kasar Kenya ta shirya wani aikin lalata kananan makamai fiye da dubu biyar da ba bisa doka ba da aka karbe daga hannun mutane, in ji wani babban jami'i a ranar Laraba.
Ministan cikin gidan Kenya, Joseph Ole Lenku, ya bayyana cewa, wadannan makamai da aka kebe domin lalatawa, an kara su kan wasu makamai dubu biyar da aka jima da karbewa, kuma aka lalata a tsawon shekaru.
Niyyar kasar Kenya na bullo da hanyoyin warware matsalolin dake nasaba da tashin hankali yanzu. Mun yi imanin cewa, muna iyar hana tashe tashen hankali da yake yake, kare rayuwar jama'a da kuma bunkasa cigaban 'dan adam, in ji mista Lenku. (Maman Ada)