in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta ba da tabbacin tsaro ga masu yawon shakatawa
2014-12-03 10:55:10 cri

Kwamitin farfado da bangaren yawon bude ido na kasar Kenya, a ranar Talatan nan ya ba da tabbacin tsaro ga masu yawon shakatawa, duk da harin ta'addancin da aka kai kwanan nan a arewacin kasar wanda ya jawo asarar rayukan mutane 60 cikin makonni biyu.

Shugabar kwamitin farfado da yawon shakatawar Lucy Karume ta ce, 'yan kwamitin nata ba za su yi kasa a gwiwwa ba wajen ganin an farfado da wannan bangare, tare da tallafawa wurare masu matukar sha'awa da dacewa a ziyarta na kasar ta Kenya, duk da barazanar tsaro da take fuskanta.

Kasar dake gabashin Afrika tana amfana daga yawon shakatawa da ake kaiwa, wadda fargaban hare-haren ta'addanci da sace baki da 'yan fashin teku na Somaliya ke yi a wuraren shakatawa na bakin ruwa, abin da ya kawo koma baya a bangaren.

Bangaren yawon shakatawa na kasar Kenya ya samu gaggarumin koma baya tun daga watan Satumban shekara ta 2011, lokacin da dakarun 'yan tawaye na Somaliya Al-Shabaab suka sace baki 'yan kasashen waje a Lamu Archipelago, da kuma ma'aikatan sa kai 'yan kasan Spaniya.

Madam Lucy Karume ta ce, 'yan tawagarta sun kidima bisa ga harin da aka kai a kan 'yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba su 36 a yankin Mandera da 'yan bindiga suka kai. Tana mai cewa, sun yi suka da kakkausar murya a kan wannan lamari na rashin imani, sannan suna da tabbaci a kan mahukuntan tsaron kasar wajen shawo kan wannan lamari yadda ya kamata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China