Shugaban kasar Benin Yayi Boni da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou za su isa a ranar yau Talata a birnin Lome bisa goron gayyatar takwaransu na kasar Togo Faure Gnassingbe, in ji wata sanarwar gwamnatin kasar.
Ziyarar shugabannin kasashen biyu na bisa tsarin bude wata tashar wucewar kayayyaki ta uku a tashar ruwar Lome, in ji sanarwar.
Wannan tasha ta uku wani gini ne mai tsawon mita 450 tare da zurfin mita 15 da wani kamfanin kasar Faransa na Bollore ya zuba kudin ginawa bisa Sefa biliyan 300 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 600, kuma wannan tasha za ta taimaka wa tashar ruwan Lome karbar manyan kwantanan dake fitowa daga yankin Asiya.
Tashar ruwan Lome na da babban matsayi ga kasashen da ba su da iyaka da teku, musammun ma Burkina Faso, Mali da Nijar inda hada-hadar shige da ficen kayayyaki ta cimma fiye da kashi 20 na yawan ayyukan wannan tashar ruwan a matsayin tashar ruwa mai zurfi guda ga yammacin Afrika. (Maman Ada)