Dubban mazauna kauyen Chibok a jihar Bornon dake arewa maso gabashin Nigeriya sun tsere daga gidajensu a ranar Jumma'an nan sakamakon farmakin da 'yan kungiyar Boko Haram ta kai kauyen baki daya.
Garin Chibok dai nan ne aka kwashe 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 yau watannin 7 ke nan, har yanzu ba labarinsu.
Mazauna garin sun ce. 'yan kungiyar sun far ma garin ne a daren Alhamis, suka bude wuta kan jama'a. A cewar Simeon Bala, wani mazaunin garin wanda ya gane wa idon shi faruwar hakan, ya ce, 'yan kungiyar sun cinna wa gidaje da dama wuta, abin da ya tilasta wa mazauna tserewa cikin daji don tsira da ransu.
Ali Ndume, 'dan majalissar dattawa dake wakiltar kudancin Borno shi ma ya tabbatar da faruwan hakan, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su inganta tsaro, tare da ba da kariya ga al'ummar Chibok.
Ya ce, 'yan kungiyar sun kai farmaki ne kasa da awa daya da janye sojojin dake sintiri a wajen, sai dai hukumar tsaro ta musanta hakan, tana mai cewa, ba janyewa aka yi ba, an je wani bangaren ne don ci gaba da aiki.
Hukumomin tsaron su tabbatar da cewa, za su ci gaba da aiki, har sai sun kwato wurin da 'yan kungiyar suka kwashe. (Fatimah)