in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kaddamar da hari kan wani ofishin 'yan sanda a Nigeria
2014-11-05 14:03:20 cri

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani hari a kan wani ofishin 'yan sanda dake jihar Gombe a arewa maso gabashin Nigeria, inda suka kutsa kai cikin ofishin 'yan sandan bayan da suka sami galaba a kan jami'an tsaron dake aiki, kuma nan take suka wawashe makaman dake cikin ofishin.

Wata majiya ta tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, wasu gungun 'yan bindiga masu dauke da muggan makamai sun kai hari a garin Nafada, dake arewacin jihar ta Gombe, inda suka kone ofishin 'yan sandan, bayan sun yi wa jama'ar garin da jami'an tsaro rashin mutunci.

Majiyoyi na tsaro sun bayyana cewar, akwai yiwuwar wasu mutane sun sami rauni a yayin da 'yan Boko Haram din suka dinga yin harbi kan mai'uwa da wabi.

Masu duba al'amuran yau da kullun sun ce, kungiyar Boko Haram ta kara kaimin ayyukanta a makonni biyu da suka shige, hakan ana ganin yana nufin ba za su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ba, kamar yadda dama suka yi aniya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China