Manzon musamman na MDD a Somaliya Nicholas Kay, ya yi gargadin cewa, akwai sama da mutane miliyan 1 da ba su da abin saka wa a bakin salati, duk da ci gaban da aka samu a kasar a bangaren siyasa da tsaro.
Jami'in na MDD ya bayyana hakan ne yayin da yake yiwa kwamitin sulhu na MDD bayani game da yanayin da ake ciki a kasar da ta shafe tsawon lokaci tana fama da rikici.
Mr. Kay ya ce, duk da galaban da aka samu a kan kungiyar Al-Shabaab, akwai bukatar gwamnatin kasar da abokan huldarta na ketare su dauki matakan da suka dace cikin gaggawa a bangaren tsaro, ci gaba, bangarorin siyasa da jin kai.
Bugu da kari wajibi ne a dama da mata da matasa cikin matakan sulhunta al'ummomin kasar tare da kafa gwamnatocin shiyyoyi na wucin gadi.
Daga karshe yana fatan za a bullo da wata sabuwar taswirar tarayyar Somaliya ya zuwa karshen wannan shekara tare da hanzarta kafa hukumar zabe mai zamanta da kuma hukumar shata kan iyaka. (Ibrahim)