Shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou ya yi kira a ranar Laraba a birnin Cotonou ga jama'ar Nijar da Benin da su ba da hadin kai kan aikin gina layin dogo da zai hade kasashen biyu. Ina yin kira ga al'ummomin Nijar da na Benin da su nuna goyon baya ga babban aikin gina layin dogon da zai hada Benin da Nijar. Wannan aiki zai karfafa musanyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, cudanya tsakanin al'ummomin kasashen biyu, da kuma taimakawa yunkurin cigaban kasashen biyu, in ji shugaba Mahamadou.
Da yake magana a yayin wani zaman taron aiki tare da shugabanni na matakai daban daban da wannan batu ya shafa, shugaban Nijar ya jaddada cewa, yana da imanin ganin ya kaddamar da bude hanyar layin dogon dake hada Niamey da Dosso, mai tsawon kilomita 140, a ranar 18 ga watan Disamban shekarar 2014.
A bangaren kasar Benin, ministan aiki da gine-gine na kasar Benin, Ake Natonde, ya ce, za'a kammala aikin sake farfado da hanyar layin dogo ta Cotonou-Parakou, mai tsawon kilomita 450 a cikin watan Satumban shekarar 2015.
Gina layin dogon da zai hada Cotonou da Niamey na cikin tsarin babban aikin gina hanyar jirgin kasa da za ta hada manyan biranen biyar na shiyyar, wato Abidjan, Ouagadougou, Niamey, Cotonou da Lome, kuma aikin zai lakume Sefa biliyan dubu daya kwatankwacin dalar Amurka biliyan biyu. (Maman Ada)