in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yammacin Afirka na kan turbar bunkasa ta fannin tattalin arziki, in ji ministan kudin Ghana
2014-10-28 10:36:18 cri

Ministan ma'aikatar kudin kasar Ghana Seth Terkper, ya ce, kasashen dake yammacin Afirka na kan kyakkyawar turbar samun karin bunkasuwa ta fuskar tattalin arzikinsu, duk kuwa da irin hasashen koma baya da ake yi kan hakan.

Wannan tsokaci na Mr. Terkper dai ya biyo bayan wani sakamakon bincike, da wata cibiyar lura da harkokin tattalin arziki mai suna S&P ta fitar, wanda ke nuni ga koma bayan da wadannan kasashe suke fuskanta a baya bayan nan.

A cewar Terkper, wancan bincike na S&P na nuni ne ga matsayin da kasashen yankin ke kai a 'yan watannin baya, wanda ya shafi irin matsalolin da suka fuskanta a lokacin, amma bai shafi halin da suke ciki a yanzu haka ba.

Terkper ya kara da cewa, yanzu haka kasashen yammacin Afirka na daukar karin matakan bunkasa, ciki hadda samar da tallafin saukaka rayuwa, da inganta albashi da alawus na 'yan kwadago, tare da batun daidaita aiwatar da manufofin asusun ba da lamuni na IMF. Baya ga batun iskar gas da kasashen ke dada samu, wanda kuma ke tallafawa farfadowarsu.

Ko da yake dai ministan ma'aikatar kudin kasar ta Ghana ya amince cewa, akwai rashin daidaito tsakanin manufofin samar da ci gaba masu gajeren zango da na matsakaitan zango, a hannu guda ya bayyana yakinin cimma nasarar daidaituwar hakan a nan gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China