in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kakkausar suka game da harin ta'addanci a Kenya
2014-11-25 20:21:42 cri
Kasar Sin ta bayyana firgici tare da suka da kakkausar murya bisa ga harin ta'addancin da ya faru a kasar Kenya.

A ranar asabar din da ta gabata ne aka kai hari a kan wata motar fasinja a arewacin kasar wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 28。

Hua Chunying kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a ganawar ta da manema labarai ta ce, Sin a ko da yaushe tana adawa da duk wani nau'in ta'addancui. Don haka ta firgita ainun game da harin da ya faru tare da suka akansa.

Kakakin ta mika ta'aziyar gwamnatin kasar Sin ga iyalai da al'ummar kasar Kenya dangane da wannan lamari.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China