in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi allawadai da harin ta'addancin da ya halaka mutane 28 a Kenya
2014-11-25 13:20:32 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan wata motar daukan fasinja a ranar Asabar a Mandera, birnin dake arewa maso gabashin kasar Kenya dake kan iyaka da kasar Somaliya, harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla ishirin da takwas. Mista Ban na isar da ta'aziyarsa zuwa ga iyalan mamatan, tare da kuma bayyana goyon bayansa ga al'umma da gwamnatin kasar Kenya, a cewar wata sanarwa da aka fitar a shafin internet na MDD.

Magatakardan MDD ya yi alkawarin cewa, MDD za ta cigaba da tallafawa Kenya da kasashen dake yankin kan kokarin da suke daga dukkan fannoni wajen da annobar ta'addanci.

Haka kuma yana fatan, za a gurfanar da masu hannu kan wannan harin da aka kai yau gaban koliya cikin gaggawa, in ji mista Ban. Kungiyar kishin islama ta Al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, kungiyar da ta kai hare hare da dama a kasar Kenya, tun cikin watan Oktoban shekarar 2011, ranar da a cikinta kasar Kenya ta tura sojojinta a kasar Somaliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China