Mataimakin darekta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO Mr. Bruce Aylward ya ce, yaduwar cutar Ebola ta ja baya a kasashen Afrika ta yamma inda a yanzu an kusa kaiwa ga mataki na tabbatar da cewa, kashi 70 na wadanda suka kamu da cutar ana killace su.
Mr.Aylward ya ce, koma bayan yaduwar cutar ya biyo bayan tsai da wasu sharudda da hukumar lafiya ta duniya da kuma tawagar matakan gaggawa a kan cutar Ebola na MDD suka yi domin dakile yaduwar cutar.
A karkashin sharuddan da aka yiwa lakabi da 70-70-60, ana faffutukar ganin kashi 70 bisa dari na mutanen da suka kamu da cutar, an killace su tare da ba su magani, kana kuma kashi 70, na wadanda suka rasu a sakamakon cutar ana rufe gawawwakinsu, ta yadda ba za su yada ba, ya kamata kuma duk za'a yi hakan a cikin kwanaki 60 tun daga farkon watan Oktober zuwa 1 ga watan Disamba.
Mataimakin darektan na WHO ya ci gaba da shaidawa 'yan jarida cewar, watanni 2 da suka shude, cutar na yaduwa kamar wutar daji a wurare da dama, to amma bayan da kasashen duniya da kuma kasashen na Afrika ta yamma suka tashi gadan-gadan, sai ga shi an samu kaiwa ga nasarar dakile yaduwar cutar ta Ebola. (Suwaiba)