Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sierra Leone, tare da hadin gwiwar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta bukaci taimakon 'yan jarida wajen yaki da cutar Ebola, in ji kungiyar 'yan jarida ta kasar Sierra Leone (SLAJ). A cikin wata wasikar da aka aikewa 'yan jaridar a cibiyar taron jama'a ta Gbonda dake Bo, jami'in kiwon lafiya mista Alhaji Turay ya bayyana cewa, babu wata hukuma ko wani mutum dake iyar karfafa aikin fadakarwa ba tare da hada kai da kafofin watsa labarai ba, haka kuma tare da ba da kwarin gwiwa ga 'yan jarida da su baiwa ma'aikatar taimako da huldar da ta bukata. (Maman Ada)