Ministan tsaron kasar Chadi Benaindo Tatola ya isa birnin Bangui na Afrika ta Tsakiya domin shirin janyewar sojojin kasar Chadi dake cikin tawagar kasa da kasa ta wanzar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya a karkashin nahiyar Afrika (MISCA), aka fara janyewar tun ranar Jumma'a da ta gabata.
Gwamnatin Chadi ta dauki niyyar janye sojojinta domin mai da martani, a cewar hukumomin N'Djamena, kan wani kamfe da ake yi na bata sunan sojojin kasar Chadi.
Wani rukunin farko dake kunshe da sojoji 200 ya bar Afrika ta Tsakiya a ranar Jumma'ar da ta gabata, inda kasar Chadi ta tura kimanin sojoji 850 a cikin aikin tagawar MISCA dake da jimillar sojoji 6000 wadanda ke kokarin maido da zaman lafiya a cikin wannan kasa da ta fadi cikin rikicin siyasa da addini. (Maman Ada)