in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin sojojin ruwan rakiya na 16 na Sin ya isa Senegal
2014-05-15 10:47:36 cri

Rukunin sojojin ruwa na rakiya na 16 na kasar Sin, dake kunshe jiragen ruwa soja biyu da jirgin ruwar kayayyaki daya, ya yada zango a ranar Laraba a kasar Senegal, hakan karo na farko ne a cikin wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika.

Rukunin sojojin ruwan na rakiya, dake gudanar da wani rangadin kasa da kasa, ya samu babban tarbo daga 'yan kasar Sin dake zauna a Senegal, 'yan makaranta, dalibai, sojojin ruwa da ma'aikatan kasar Senegal.

Kafin wucewarsa da aka tsai da a ranar Jumma'a mai zuwa, rukunin sojojin ruwan rakiya na kasar Sin zai samu ziyayar masu kallo da dama, da kuma gudanar da ayyukan horaswa tare da sojojin ruwan kasar Senegal da shirya ziyarar gani da ido kan wadannan jiragen ruwan soja na kasar Sin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China