in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen yakin Libya na luguden wuta kan filin jirgin saman Mitiga dake Tripoli
2014-11-25 15:45:48 cri

Jiragen yaki na rundunar sojojin kasar Libya sun yi luguden wuta a ranar Litinin kan filin jirgin sama na Mitiga dake birnin Tripoli, a cewar wasu majiyoyin soja. Hare haren ta sama kan muhimmin filin jirgin na da manufar yanke hanyar isar da abinci da kayayyaki ga mayakan kungiyar Aube ta Libya, in ji komandan din sojojin sama, janar Saqr Jeroshi, tare da bayyana cewa, sararin saman libya a bangaren gabas da yamma a halin yanzu suna samun kariya yadda ya kamata daga jiragen yaki na kasar Libya.

Jiragen yaki samfurin MIG-21 da suka tashi daga sansanin sojojin sama na Al-Watia, mai tazarar kilomita 150 daga birnin Tripoli ne suka kai wadannan samame, in ji wata majiyar tsaro. Rundunar sojojin kasar tare da taimakon mayakan sa kai masu sassaucin ra'ayi ta gudanar da wasu samame bisa burin karbe mulkin garuruwan da suka rasa. Tsawon makwanni biyu na baya bayan nan, an samu musanyar wuta da tashe tashen hankalin da suka yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 356 a Benghazi. Haka kuma a ranar Lahadi, rundunar sojojin kasar Libya ta yi kira 'yan kasar da su kaucewa yankunan fagen a yayin da take kokarin gudanar da ayyukan soja na kwato babban birnin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China