in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bukatar Sin a bangaren mai zai ragu a shekarar 2030
2014-11-13 10:43:07 cri

Hukumar kula da makamashi ta kasa da kasa (IEA) ta bayyana a ranar Laraba cewa, bukatar da kasar Sin ke da shi a bangaren mai zai dan ragu a tsakanin shekarar 2030, ko da ya ke zai zarce na kasar Amurka a matsayinta na kasar da ke kan gaba wajen sayen mai a wannan lokaci.

Babbar darektar hukumar Maria Van der Hoeven ce ta bayyana hakan yayin gabatar da rahoton da hukumar ta IEA ta fitar na wannan shekara a birnin Landan, inda hukumar ta yi gargadin cewa, za a fuskanci kalubale na dogon lokaci a tsarin na makamashi.

Rahoton ya ce, akwai yiwuwar man da ake samarwa zai karu zuwa ganga miliyan 104 a kowace rana a shekara 2040, amma hakan zai haifar da babbar matsala a harkar zuba jari a yankin Gabas ta Tsakiya.

A halin da ake ciki kuma, karuwar bukatar man a duniya za ta ragu a shekara ta 2040, ganin yadda bukatun kasashen da ke kan gaba wajen sayan man, ko bukatun nasu ya ragu ya zuwa shekara 2040, ko kuma sun kai kololuwar bukatar tasu kamar Amurka, kungiyar tarayyar Turai da Japan da kuma kasashen Sin, Rasha da Brazil a hannu guda.

Sai dai kuma ana ganin kasar Indiya da yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da yankin Gabas ta Tsakiya da kudu maso gabashin Asiya suna daga cikin yankunan da za su kasance cibiyar bunkasuwa.

Rahoton na IEA ya kuma ce, wannan batu zai haifar da karuwar ma'aikata da kashi 60 cikin 100 ya zuwa shekara ta 2040. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China