Wata sanarwa daga ma'aikatar lura da harkokin da suka shafi hulda da kasashen ketare ta Afirka ta Kudu, ta bayyana aniyar kasar game da karfafa dangantakar hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin, karkashin manufofin bunkasa kawance da amincewar juna da kasashen 2 suka cimma.
Wani jami'in hukumar ta DIRCO ne ya fitar da sanarwar a jiya Laraba, jim kadan da isowar minista mai kula da ma'aikatar Maite Nkoana-Mashabane nan birnin Beijing, domin halarci taron hadin gwiwar ma'aikatun kasashen biyu.
Sanarwar ta ce, taron na wannan lokaci zai ba da damar nazartar al'amuran da suka biyo bayan yarjejeniyoyin da jagororin kasashen suka rattabawa hannu a watan Maris na shekarar da ta gabata.
Kaza lika za a yi amfani da taron na ranekun Laraba da Alhamis, wajen nazartar batun zartas da ayyuka da aka amince da su, da kuma bincikar kalubalolin da aka fuskanta, baya ga kokarin warware matsalolin da aka ci karo da su, duka dai da nufin bunkasa hadin kan kasashen ta fuskar tattalin arziki.
Da yake karin haske game da hakan, kakakin DIRCOn Clayson Monyela, ya ce, babbar manufar Afirka ta Kudu game da hakan ita ce, amfani da dukkanin dama, wajen samar da daidaito da yaki da fatara da karancin ayyukan yi tsakankanin al'ummarta. (Saminu)