Wani zaman taro na kwanaki biyu kan tsaron cikin gida ya bude a birnin Abuja a ranar Talata, bisa manufar cimma hanyoyin karko kan rikicin kungiyar Boko Haram da sauran wasu matsalolin tsaro dake kasar Najeriya ke fuskanta a halin yanzu. Dandalin, mai taken "dunkulewar tsaron jama'a a Najeriya" da cibiyar manufofin kasa (NOA) ta shirya, an yi bikin bude shi a karkashin jagorancin tsohon sakatare janar na kungiyar Commonwealth, mista Emeka Anyaoku. A cewar tsohon jami'in Commonwealth, a Najeriya, addini ya kasance wani babban ginshiki dake taimakawa rikicin Boko Haram, kungiyar ta'addanci dake fatan kafa shari'ar musulunci a wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika.
Wasu mahalarta wannan taro, kamar wakilan rundunar sojojin Najeriya da na wasu hukumomin tsaro, sun jaddada cewa, bukatar Najeriya da abokan huldarta na kasa da kasa shi ne na tashi tsaye domin fuskantar kalubalolin ta'addanci da wasu matsalolin tsaron cikin gida. Za'a kammala taron a ranar Laraba, idan mahalarta taron suka bullo da wani tsari domin tsaron jama'a a Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afrika. (Maman Ada)