in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da kasashen duniya wajen yaki da cin hanci da rashawa
2014-11-27 17:21:10 cri

A wannan shekarar da muke ciki, kasar Sin tana ta kara azama wajen hukunta laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa, a hannu guda kasar na inganta hadin gwiwarta da gwamnatocin kasashen duniya, wajen farautar masu aikata cin hanci dake tserewa kasashen waje, da kwato kudaden da suka sata. Sauran matakan sun hada da mai da irin wadannan mutane gida daga kasashen da suke samun mafaka. A jiya Laraba ne kuma wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya, da su zage damtse tare da kasar Sin, wajen daukar matakan shari'a domin yaki da laifukan cin hanci da rashawa.

Tun bayan da kasar Sin ta maido da Zhang Zhenhai, wanda aka zarga da aikata laifin fashin jirgin sama daga kasar Japan, a watan Afrilu na shekarar 1990, wanda ya zama karo na farko da kasar Sin ta samu nasarar tirsasa maido da masu aikata laifuka zuwa gida, ya zuwa yanzu, an kama masu aikata manyan laifuka da dama da suka tsere zuwa ketare, ta hanyar kamo su daga kasashen da suke fakewa, bisa hadin gwiwar ma'aikatar harkokin wajen kasashe, da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.

A yayin taron manema labarun da aka shirya a ranar 26 ga wata, shugaban sashen kula da ka'idoji na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Xu Hong, ya bayyana cewa, tun bayan shekaru 80 na karnin da ya gabata, ma'aikatar ta fara hadin gwiwa tare da ofisoshin jakadanci na Sin da ke kasashen waje, domin farautar masu cin hanci da zamba, dake tsallakewa zuwa ketare, da kwato kudaden da suka sata.

Mr. Xu ya kara da cewa daya daga cikin muhimman ayyukan ma'aikatar harkokin wajen Sin a wannan fanni shi ne, gudanar da shawarwari, da kuma daddale yarjejeniyar shari'ar kasa da kasa, a kokorin aiwatar da wannan tsarin bisa doka. Xu Hong ya kara da cewa,

"Kasancewar masu aikata laifufuka a kasar Sin su kan gudu zuwa kasashe masu ci gaba da ke yammacin duniya, ya sa ma'aikatar harkokin wajen Sin ta himmatu, wajen daddale yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin shari'a da wadannan kasashe. Daga baya kuma, Sin ta kulla yarjejeniyoyi tare da kasashen Faransa, da Sifaniya, da Australia, da Italiya da Portugal, kan yadda za a tiso-keyar masu aikata laifufuka daga kasashen da suke samun mafaka, baya ga daddale yarjejeniyoyi tare da kasashen Amurka, da Canada, da Faransa, da Sifaniya, da Portugal, da Australia, da New Zealand, da Birtaniya da Belgium, kan yadda za a ba da tallafi wajen yanke hukunci kan masu aikata manyan laifufuka."

Ya zuwa watan Nuwambar na bana kuma, kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyi 39 tare da sauran kasashen duniya ta fuskar dawo da masu aikata laifufuka daga kasashen da suke samun mafaka zuwa gida, inda tuni aka fara aiwatar da 29.

Haka zakila, yawan yarjejeniyoyin ba da tallafi a fannin hukunta masu aikata manyan laifufuka da kasar Sin ta kulla tare da sauran kasashe ya kai 52, ciki hadda 46 da tuni aka fara aiwatarwa.

Wani abin lura ma dai shi ne, kasar Sin ta riga ta kammala shawarwari tare da kasar Canada, kan yarjejeniyar tiso-keyar masu aikata cin hanci, da maido da dukiyoyin da suka diba zuwa gida Sin. Yarjejeniyar da ta kasance irinta ta farko da Sin ta yi a wannan fanni. Ana kuma hasashen cewa, wannan mataki na da babbar ma'ana ga aikin hadin gwiwar Sin da kasashen waje a wannan fanni.

Bugu da kari kasar Sin ta riga ta yi shawarwari tare da Amurka da Canada kan hadin gwiwarsu a fannin yanke hukunci, wanda ya samar da muhimmiyar hanya ga aikin farautar masu ci hanci dake gujewa kasashen su zuwa ketare, da kwato kudaden da suka sata. Game da hakan Xu Hong ya ce,

"A watan Mayu na shekarar 1998, an kafa kungiyar hadin kan Sin da Amurka a fannin yanke hukunci. Kana Sin ta ci gaba da dora muhimmanci kan ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a karkashin wannan tsari, har ma ta samu nasarar tiso-keyar wasu da suka aikata laifukan cin hanci daga Amurka zuwa gida, tare da gurfanar da su a gaban kotu. Bugu da kari, kasashen Sin da Canada sun samu kyawawan sakamako wajen hadin giwa a fannin shari'a. Alal misali, kasar Sin ta dawo da Lai Changxiang daga kasar Canada, bayan da ya aikata laifin fasa-kwauri ya kuma tsere tsawon shekaru 12."

Ban da wannan, Xu Hong ya ce yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta MDD, da kuma kwamitocin zartaswa na kungiyar APEC da na G20, kan yaki da cin hanci da rashawa, dukkaninsu na da irin wadannan tsare-tsare na sa kaimi kwarai ga kasashen duniya, wajen gudanar da hadin gwiwa a fannin farautar masu aikata laifukan cin hanci dake guduwa zuwa ketare, da kwato kudaden da suka sata.

Duk da ci gaban da aka samu, sakamakon bambancin tsarin al'umma da na shari'a, hadin gwiwar kasashen duniya na yaki da cin hanci na tinkarar babban kalubale. Xu Hong ya bayyana cewa,

"Ya zuwa yanzu, kasar Sin ba ta kulla wata yarjejeniya tare da Amurka kan tirsasa maido da masu aikata irin wadannan laifufuka ba. Bisa dokar Amurka, ba za a iya gudanar da ayyukan hadin gwiwa a wannan fanni ba, sai dai bayan kulla yarjejeniya game da hakan. Don haka babu abin da za a iya yi illa bin wasu sauran hanyoyi, kamar dawo da su daga Amurkan bisa hujjar shiga kasar ta barauniyar hanya, da kuma gurfanar da su a Amurka, domin fuskantar shari'a a can. "(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China