Shugaban kasar Zambiya, Michael Sata ya tunbuke ministansa na shari'a, Wynter Kabimba. Haka kuma an kori shi Kabimba daga mukaminsa na sakatare janar na jam'iyyar FP mai mulki, in ji fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwar da aka aike wa jaridun kasar a ranar Alhamis, ba tare da ba da wani karin haske ba kan wannan mataki.
Ministan tsaron kasar Edgar Lungu ne, zai rike kujerar ministan shari'a da ta sakatare janar na jam'iyyar FP. (Maman Ada)