Shugaban wucin gadi na kasar Zambiya, Guy Scott, ya sanar a ranar Talata cewa, zaben shugaban kasar zai gudana a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2015. Za'a dai shirya wannan zabe bayan rasuwar shugaba Michael Sata a ranar 28 ga watan Oktoba a asibitin King Edward VII dake birnin London, inda ya je domin binciken lafiya. Kundin tsarin mulki na wannan kasa ya tilasta shirya wani zaben shugaban kasa a cikin kwanaki 90 idan babu kowa kan wannan kujera. Shugaban kasar Zambiya mai tafiyar da mulkin wucin gadi a halin yanzu ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a ofishinsa cewa, shirya wannan zabe na daidai da kundin tsarin mulkin kasar Zambiya. (Maman Ada)