Kwamitin tsaro na MDD a jiya Laraba ya cimma matsaya a kan Libya, tare da yin kira da a dakatar da bude wuta nan take, sannan kuma ta kara tsaurara takunkumin da ya hada da wadanda ke da hannu a cikin wannan tashin hankali.
A cikin wata amincewa da aka yi gaba daya, kwamitin mai mambobi 15 ya yi kira ga dukkan bangarori da su dakatar da bude wuta a tsakanin su, sannan su kawo karshen fada. Yana mai nuna cikakken goyon bayan ga kokarin MDD a kan kasar ta Libya, da kuma wakilin babban magatakardar majalissar a game da hakan.
Kwamitin ya kuma yi suka game da amfani da karfin tuwo a kan fararen hula da hukumomin fararen hulan inda ya yi kira ga wadanda ke da hannu a ciki da su dauki alhakin wannan danyen aiki.
Har ila yau kwamitin tsaron MDD ya tsai da shawarar cewa, takunkumin da aka kakabawa kasar ta Libya a zaman shi na baya, yanzu zai hada har da wadansu mutane da cibiyoyi da suke da hannu ko taimakawa duk wani nau'in aikin dake barazana ga zaman lafiya, daidaito da kuma tsaron kasar ta Libya, ko kuma ya kawo cikas ga shirin komawa ga mulkin demokradiya cikin lafiya.
Haka kuma kwamitin ya yi kira ga dukkan mambobin majalissar da su hada kai don ganin an cimma burin da aka saka a gaba da suka hada da karfafa, gyara, daidaita ko dage matakan, sannan kuma da shirin sake duba manufofin ofishin majalissar a kan harkokin Libya yadda ya kamata a kowane lokaci domin samar da cigaba a kasar ta Libya. (Fatimah)