in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin kasuwancin Afrika na shirin kaddamar tsarin biya ta hanyar waya
2014-11-06 15:24:47 cri

Bankin kasuwancin Afrika (Afreximbank) ya bayyana cewa, yana aiki kan shirin shigar da wani tsarin biya ta hanyar waya domin tallafawa kasuwanci da harkokin biya tsakanin 'yan Afrika, in ji wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta a ranar Laraba.

Jean-Louis Ekra, shugaban bankin ya bayyana wa wakilai mahalarta zaman taro na kwanaki uku a birnin Lusaka cewa, nasarar shigar da tsarin zai samar fiye da dalar Amurka biliyan hamsin na kasuwancin shiyya. Haka kuma bankin na aiki tare da gungun Econet Wireless domin bunkasa da shigar da tsarin, in ji mista Ekra tare da nuna cewa, kimiyya da fasaha na kasancewa wasu muhimman hanyoyin gudanar da hada hadar kudi a Afrika, da ma duniya baki daya.

Taron da Afreximbank ya shirya tare da hadin gwiwar bankin Zambiya a birnin Lusaka, na da manufar baiwa mahalarta kwarewar tafiyar da tsare tsaren yarjejeniyoyin kudi da ke iyar janyo kudi. Haka kuma wata hanya ce ta taimakawa warware matsalolin samar da kudaden gudanar ayyukan ci gaba da kuma kasuwanci da ake samu a Afrika, tare kuma da tallafawa ci gaban kasuwanci da tattalin arzikin nahiyar cikin dogon lokaci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China