in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsatataccen masana'antu mafi muhimmanci ne ga Afrika wajen tsallake tsoffin na'urori
2014-11-21 10:35:26 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Alhamis din nan 20 ga wata ya ce, Afrika tana bukatar kore, tsabtataccen masana'antu domin tsallake tsofaffi na da, gurbataccen ayyukan da yadda ake tafiyar da su domin samun anfana daga sabbin fasahohi.

Mr. Ban yana magana ne domin ranar masana'antun Afrika na bana, mai taken "ci gaba mai dorewa da za'a shiga: ci gaban fasahar masana'antu da tsaron abinci'' wanda ya mai da hankali ne a kan dangantaka tsakanin noma da ci gaba.

Ya ce, noma har yanzu babban bangare ne a samun kudin shiga ga al'umma, kuma yana rike da kashi 60 cikin dari na kwadagon Afrika, musamman ga mata.

Sai dai kuma, rashin samar da isassun amfanin gona har yanzu yana barazana ga abinci a nahiyar Afrika baki daya. Duk da tattalin arzikin sauran kasashen Afrikan ya farfado a 'yan shekarun nan, karuwan ci gaba ba ko da yaushe yake zama samar da arziki ba.

Shigar da kuma ci gaban masana'antu wani babban jigo ne na zuwa gaba domin a samar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki, samar da abinci da kuma yaye talauci a Afrika, in ji shi.

Babban magatakardar ya ba da tabbacin MDD na inganta shigar da kuma dawwamar da ci gaban masana'antun don taimaka wa Afirka a bangaren hauhawar tattalin arziki, da cudanya cikin walwala. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China