in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ebola ta fadada matsalar karancin abinci, in ji UNDP
2014-11-25 11:03:22 cri

Wani rahoto da shirin samar da ci gaba na MDD UNDP ya fitar, ya bayyana matukar bukatar daukar karin matakan shawo kan matsalar karancin abinci a kasashen da suka sha fama da cutar Ebola.

Rahoton ya bayyana yadda wannan cuta ta haifar da hauhawar farashin kayan abinci a wadannan kasashe na yammacin Afirka, lamarin da ya sa magidanta da dama ba sa iya mallakar isasshen abinci domin ciyar da iyalan su.

Hakan, a cewar babban jami'in shiyya mai lura da harkokin tattalin arziki na shirin UNDP Ayodele Odusola, wanda kuma shi ne ya gabatar da rahoton, sakamako ne na karancin abinci a kasuwanni, da kuma kalubalen da harkokin noma suka fuskanta, sakamakon rufe kan iyakoki, da ma sauran dalilai.

Odusola ya kara da cewa, bullar cutar Ebola ya haifar da raguwar sayayyar kayan abinci da kaso 20 cikin dari a kasar Saliyo, adadin da ya kai kaso 25 bisa dari a Liberiya.

Wannan rahoto ya kuma bayyana yankunan karkara, a matsayin wuraren da wannan matsala ta fi shafa, sakamakon tsadar sufuri, da kuma raguwar ribar da ake samu daga noma a irin wadannan yankuna. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China