Kwamitin tsaron MDD ya yi na'am da bayyana sakamakon zaben 'yan majalissun wakilan kasar Libya, tare da kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a kasar, da su rungumi hanyoyin samar da daidaito tsakanin al'ummun kasar.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamitin tsaron ya fitar a jiya Laraba. Kaza lika sanarwar ta bukaci a gaggauta fara gudanar da zaman majalissar wakilan, domin tinkarar muhimman ayyuka, da suka hada da cimma daidaito kan ayyukan gwamnati, da dora kasar kan turbar dimokaradiyya mai nagarta.
Kwamitin mai wakilai 15, ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan da kasashen duniya ke baiwa gwamnati da sauran sassan hukumomin kasar ta Libya, a kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kwamitin shirya zabe a kasar, ya fidda sakamakon zaben 'yan majalissun wakilai da aka gudanar ran 25 ga watan Yuni, matakin da ake zaton na iya haifar da takaddama, tsakanin masu sassaucin ra'ayi da bangaren masu kaifin kishin Islama a kasar. (Saminu)