Tawagar MDD da ke Sudan ta Kudu (UNMISS) ta bayyana cewa, tashin hankali na ci gaba da shafar fararen hula a Sudan ta Kudu, yayin da majalisar ta samu rahoton da ke nuna cewa, dakarun adawa sun kaddamar da wani hari, inda suka kama tsaunin Dolieb dake kudancin Malakal a jihar Upper Nile.
Kakakin MDD Farhan Haq wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya kuma ce, akwai karin rahotannin da ke nuna cewa, dakarun adawa sun kara nausawa zuwa Malakal, babban birnin jihar Upper Nile, kafin daga bisani sojojin kwatar 'yancin Sudan (SPLA) su fatattake su.
Bugu da kari tawagar ta UNMISS ta ce, an ji karar manyan abubuwan fashewa na fitowa daga tsaunin Dolieb, ko da yake majiyoyin SPLA sun shaidawa tawagar ta UNMISS cewa, dakarun gwamnatin sun sake kwace tsaunin na Dolieb, kana sun danna dakarun adawa zuwa gabar kogin Sobat daga kudu.
Bayanai na nuna cewa, kimanin mutane 100,000 ne da suka rasa gidajen su ke tsugune a sansanonin tawagar ta UNMISS da ke sassan daban-daban na kasar Sudan ta Kudu. (Ibrahim)