in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya yaba da nasarar zabe a Guinea-Bissau
2014-05-23 10:13:00 cri

Jakadan kasar Sin dake kasar Guinea-Bissau, Wang Hua, ya yaba a ranar Alhamis da nasarar gudanar da zabe a cikin wannan kasa.

Wannan wani muhimmin mataki ne domin kara karfafa kafuwar tsarin demokaradiyya a kasar Guinea-Bissau, in ji jami'in diplomasiyyar kasar Sin yayin wani bikin ba da taimako ga gwamnatin kasar Guinea-Bissau.

A cewar mista Wang Hua, nasarar wannan zabe ta samu tushe ne daga halartar jama'ar kasar sosai, da kuma kishin al'ummar kasar.

Mista Wang Hua, ya jaddada alkawari da babbar niyyar gwamnatin kasar Sin na cigaba da tallafawa kasar Guinea-Bissau.

A shirye muke, mu yi aiki tare da sabbin hukumomin da aka zaba ta hanyar demokaradiyya domin gina wata sabuwar kasar Guinea-Bissau domin jin dadin jama'ar kasashen biyu, in ji mista Wang Hua. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China