Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya shawarci hukumomin kasar Burkina Faso da su baiwa jama'a damar yin zanga-zanga saboda jama'a suna da 'yancin gudanar da taruka da zanga-zangar a cikin lumana.
Kiran na Ban Ki-moon ya biyo bayan jerin zanga-zanga a kasar ta Afrika ta yamma tun bayan da aka nada wani sabon shugaban kasar wanda ke samun goyon baya daga sojojin kasar.
Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, a yayin da magatakardan MDD ke cikin damuwa kan halin da kasar ta Burtkin Faso ta shiga, Ban Ki-moon ya kuma jaddada 'yancin kare rayukan jama'a da kaddarori.
Ban Ki-moon ya ce, sojojin kasar da jam'iyyun 'yan adawa, da sauran kungiyoyi na ci gaba da tuntubar juna, a yayin da shi kuma magatakardan MDD ya shawarci dukanin bangarorin da su daidaita a kan mika mulki a cikin kwanciyar hankali.
Shugaban rikon kwarya na kasar ta Burkina Faso Isaac Zida ya yi alkawarin mika mulki ga wata hukuma wacce za ta mai da kasar kan turbar damokradiyya. (Suwaiba)