Sabon shugaban rikon kwarya a kasar Burkina Faso, Michel Kafando ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Talata a birnin Ouagadougou, a matsayin shugaban da zai tafiyar da ragamar mulkin kasar a tsawon wa'adin shekara guda har zuwa lokacin zabubuka a cikin watan Nuwamban shekarar 2015.
"Na rantse a gaban al'ummar kasar Burkina Faso bisa mutuncina cewa, zan kare da girmama kundin tsarin mulki, da kundin wucin gadi da dokokin kasa, tare da yin iyakacin kokarin tabbatar da adalci ga dukkan 'yan kasar Burkina Faso." in ji mista Kafando, hannusa na dama dage gaban mambobin kwamitin kundin tsarin mulki.
An zabe ka a matsayin shugaban kasar Burkina Faso. Ya kamata kasance shugaban dukkan 'yan kasar Burkina Faso, in ji shugaban kwamitin kundin tsarin mulki, Albert De Millogo. (Maman Ada)